’Yan sanda sun kama babban wanda ake zargi da kisan wata matar aure masi shekaru 22 a gidanta da ke unguwar Tsamiyar Duhuwa da ke yankin Farawa a Jihar Kano.
A ranar 6 ga watan Afrilu ne aka tsinci gawar matar mai suna Rumaisa Haruna, ne a gidanta bayan an yi mata kisan gilla.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar kama wanda ake zargin mai shekaru 35 mazaunin unguwar Madatai ne a ranar 23 ga watan Mayu ta hanyar binciken sirri.
Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a hannun ’yan sanda, inda ya bayyana cewa ya shiga gidan wadda aka kashe ne ya shake ta, sa’annan ya soka mata wuka a wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.
- Gwamnatin Kano za ta sabunta masallacin da aka kona masallata 23 a kan N150m
- Amarya ta kashe uwargida da wuka a Katsina
Sanarwar ’yan sandan ta ce: “Za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.”
Lamarin mai ban tausayi ya bayyana ne lokacin da mijin matar mai suna Ibrahim Mohammed, ya tsinci gawarta da mummunan rauni a wuyanta. An garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.
Rundunar ’yan sandan ta yaba wa jami’anta masu bincike saboda kwarewarsu da kuma jajircewarsu wajen cafke wanda ake zargi, inda ta kara da cewa ana ci gaba da bincike don tabbatar da an yi cikakken adalci.