Hukuma ta cafke wani mai wa’azin Musulunci kuma shugaban makarantar addini kan laifin batanci ga addinin Islama da kuma cakuda mata da maza a sahun Sallah a kasar Indonesia.
Malamin mai suna Panji Gumilang, yana kuma fuskantar zargin halasta wa mata yin huduba da limancin Sallar Juma’a makarantar kwana ta Musulunci mai suna Al-Zaytun da yake jagoranta.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Hana ’Yan Najeriya Shiga Zanga-Zangar NLC
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Muke Yin Ciko —’Yan Mata
Fitar wani bidiyo da ke nuna mata da maza suna sallah a sahu daya a makarantar mai dalibai 5,000 a watan Afrilu ya jawo tofin Allah tsine da bore a kusa da harabar makarantar, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka cafke shi.
Addinin Musulunci dai ya haramta cakuduwar maza da mata, inda a sallah sahun mata ke kasancewa daban, kuma a bayan na maza; haka bai halasta wa mata huduba ko jagorancin sallar Juma’a ba.
Al’ummar kasar Indonesia wadanda yawancinsu Musulmi ne, na zargin makarantar Al-Zaytun da yada akidun da suka ci karo da koyarwa Al-Kur’ani da sunan Musulunci.
Malamain da ke tsare a hannun ’yan sanda a yanzu yana fuskantar zargin batanci, maganganun tsana da kuma yada akidun da suka saba wa koyarwar Al-Kur’ani da sunan Musulunci a makarantar.
Kakakin ’yan sandan kasar Ahmad Ramadhan ya sanar a ranar Laraba cewa sun cafke shugaban makarantar, Panji Gumilang, inda suka tsare shi na tsawon kwana 20, gabanin gurfanar da shi a gaban kotu.
Idan kotu ta sami Gumilang da laifi, za a yanke masa hukuncin daurin shekara 21 a gidan yari — 5 kan batanci, 6 na yada maganganun tsana da kuma 10 a kan tayar da zaune tsaye da gangan.
Ana kuma zargin Gumilang da makarantarsa da alaka da kungiyar Darul Islam, da ta yi yakin kafa gwamnatin Musukunci a kasar a shekarun 1950 zuwa 1960.
Tun a watan Yuni dubban mutane sun sha yin zanga-zangar neman a rufe makarantar da ke yankin Yammacin Java.
Kundin tsarin mulkin kasar Indonesia wadda yawancin al’ummarta Musulmi ne ya yi tanadin hukunci ga masu aikata batancin addini.
Sai dai a baya ba a fiye amfani da dokar ba, sai bayan mulkin soji a 1998, inda a shekarar 2017 aka yanke hukuncin daurin shekara biyu ga tsohon gwamnan birnin Jakarta na farko, wanda Kirista ne.