Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum da wasu gwamnonin Arewa da mataimakansu sun halarci taron gaggawa a jihar Kaduna.
Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar Borno sun tabbatar da cewa gwamnan jihar ya halarci taron kungiyar gwamnonin arewa, domin tattauna wasu muhimman abubuwa da ke faruwa a yankin.
- Zulum ya bukaci a tura jami’an SARS Borno
- Zanga-zanga: An baza jami’an tsaro a Kaduna
- #EndSARS: Gwamna Lalong ya sanya dokar hana fita a Filato
- ’Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar #EndSARS a Kano
Majiyar ta bayyana cewa “gwamna Zulum ya tashi zuwa Kaduna domin halartar taron gaggawa, wanda daga ciki za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi Arewa da ma kasa baki daya, musamman ma rikicin da ya shafi jihar Legas, Fatakwal da babban birnin tarayya Abuja”, inji majiyar.
Sai dai ba bayyana wa manema labarai sakamakon taron ba wanda ya gudana a daidai lokacin da sassan ke fama da rikicin da ya barke sakamakon zanga-zangar #EndSARS da ‘yan daba suka shiga.
Mahalarta taron sun hada da gwamnonin jihohin Sakkwato, Yobe, Kebbi, Nasarawa, Gombe, Zamfara da kuma Neja.
Mataimakin gwamnan jihohin Kaduna, Kano da Kogi su ma sun halarci taron.