Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa garin Marte bai koma hannun ’yan Boko Haram ba.
Zulum, ya kai ziyara garin Marte domin duba halin da ake ciki da kuma yadda za a tabbatar da zaman lafiya.
- Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su
- Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5
Kafin zuwansa, ’yan ta’adda sun sake karɓe iko da Marte bayan harin da suka kai a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka tsere zuwa garin Dikwa.
Gwamnan, ya ce mutane kimanin 20,000 ne suka tsere daga Marte, wanda hakan ka iya kawo matsala musamman ga matasa da za su iya shiga cikin harkokin ta’addanci.
Ya ce: “Muna da alhakin kare Marte. Idan muka rasa wannan gari, za mu iya rasa sauran ƙananan hukumominmu.
“Don haka ina roƙon Gwamnatin Tarayya da sojojin Najeriya su haɗa hannu wajen kare wannan gari.”
Zulum, ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Borno.