✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yan kasuwa 15 a wani sabon hari a Binuwai

Jihar Binuwai na fuskantar hare-haren 'yan bindiga a baya-bayan nan.

Aƙalla ’yan kasuwa 15 ne aka kashe a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wasu garuruwa da ke Ƙaramar Hukumar Agatu a Jihar Binuwai.

’Yan kasuwar na kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Oweto da yammacin ranar Asabar lokacin da aka kai musu hari a kusa da garuruwan Ogwumogbo da Okpo’okpolo.

Tsohon mataimakin shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu, John Ikwulono, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce mutane da dama sun jikkata.

Ya ce mutum biyar aka kashe a kusa da wani ƙaramin rafin da ake kira Abekoko.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu na yanzu, Melvin James, yana wajen jana’izar waɗanda aka kashe lokacin da manema labarai suka kira shi.

Hadiminsa ne, ya ɗauki waya, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ɗora laifin kan makiyaya masu ɗauke da makamai.

Da aka tuntuɓi sakataren Ƙungiyar Miyetti Allah na jihar, Ibrahim Galma, ya ce bai da masaniya game d harin ba amma zai bincika.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bai yi wani ƙarin haske ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton harin ba.

Wannan hari ya ƙara yawan mutanen da aka kashe a Jihar Binuwai daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 17 ga watan Mayu zuwa 174.

Sai dai mazauna yankin sun ce adadin na iya wuce haka, duba da yadda wasu hare-hare ba a kai rahotonsu ba ga hukumomin tsaro.

Yankuna da dama a jihar sun fuskanci hare-hare a baya-bayan nan, ciki har da Gwer ta Gabas, Guma, yankin Sankera (Katsina-Ala, Logo, Ukum), Otukpo, Gwer ta Yamma, Kwande, Apa, Agatu da Makurdi.

Yankin Sankera ne ya fi fuskantar hare-hare, inda aka kashe aƙalla mutum 83 tsakanin 17 zuwa 21 ga watan Afrilu kaɗai.