✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum zai saya wa sojoji da ’yan sa-kai ƙarin motoci don yaƙar Boko Haram

Gwamnan ya jaddada aniyarsa na ci gaba da yaƙi da 'yan ta'adda a jihar.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban.

Ya ce za a bai wa ’yan sa-kai motoci shida ƙirar Toyota Hilux, ciki har da CJTF, mafarauta da ’yan banga, sannan za a bai wa sojoji ƙarin motoci huɗu masu bindiga.

Zulum, ya kuma raba wa iyalai 10,000 da ke fama da talauci a yankin kayan abinci, yawancin waɗanda suka samu kayan mata da marasa galihu ne.

A garin Rann, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Kala-Balge, gwamnan ya kwana a can tare da duba lafiyar jami’an tsaro da kuma tallafa musu.

Zulum, ya ce ziyarar tana cikin ƙoƙarinsa na ƙarfafa haɗin kai da juriya a tsakanin al’ummar jihar, duba da ƙalubalen tsaro da suke fuskanta daga ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.

Ya ce, “Ina kira ga dukkanin mazauna Borno da su haɗa kai da jami’an tsaro domin kare mu daga barazanar tsaro.”

Zulum, ya kuma nuna godiyarsa ga al’ummar jihar da sauran yankuna da suka amsa kiran yin azumi da addu’a domin samun zaman lafiya.

Ya ce mutane daga wasu jihohi da ma ƙasashen waje sun haɗa kai da su wajen neman taimakon Allah domin kawo ƙarshen matsalar tsaro.