Jama’ar gari a sun yi garkuwa da matan wasu ’yan bindiga a yankin Birnin Magaji da ke Zamfara.
Matasan yankin sun yi haka ne a matsayin martani bayan da ’yan bindiga sun wasu wasu mutane yankin su bakwai a gona.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Bawali A Waje Ke Yada Cututtuka
- Gabon: Janar Brice Nguema zai karɓi rantsuwa a Kotun Koli
Sun kuma alsashi cewa ba za su saki matan ’yan bindigan da ke hannunsu ba, har sai mazajensu su sako mutanen yankin da suka sace.
Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito wani mazaunin yankin na cewa suna tsaka da juyayin sace ’yan uwansu ne sai ga matan ’yan bindiga sun zo wucewa.
“Sai mutane suka ce ba za su wuce ba kuma ba za su sake su ba, sai an kawo ‘yan uwanmu da aka kama,” in ji mutumin.
Ya ce ’yan bindigar sun kira matan nasu ta waya suka neme su da su yi kokari a sake su don suna cikin ‘mawuyacin hali’.
Wani mazaunin yankin na daban ya ce ’yan uwansu da aka sace suna tsaka da aiki a gona gungun wasu ’yan bindiga fiye da goma suka zagaye su da bindigogi, suka tafi da su.
Ya ce bayyana cewa daga baya mutum daya daga cikinsu ya dawo gida, saura maza hudu da mata biyu a hannun ‘yan bindigar.