Manyan ’yan Arewa na shirin ganawa da gwamnoni yankunan Kudu da Arewa don magance zaman dar-dar da kuma inganta hadin kai a kasar.
’Yan Arewan a karkashin inuwar Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), sun bukaci makiyaya da su koma Arewa idan ba sa cikin aminci a inda suke a yanzu, tare da jan hankalin ’ya sa kai a cikin al’ummomi da su daina barazanar da hare-hare.
- Sojoji ne ba sa so yaki da ta’addanci ya kare —Sheikh Gumi
- Dole ce ta sa makiyaya suka fara amfani da AK-47 – Gwamnan Bauchi
- Kwankwasiyya ta soki Ganduje kan yunkurin rushe gadar sama
- Dalibin aji hudu ya lashe gasar musabakar Al-Qur’ani a Kebbi
“Dattawan Arewa sun yi alkawarin ci gaba da aiki don kwato kasar nan daga mawuyacin halin da mutane marasa kishi suka sanya ta, yawancinsu suna kan mukamai,” inji kungiyar
“Mun shirya ganawa da gwamnonin Arewa da na Kudu don inganta kyakkyawan hadin gwiwa; muna kuma da niyyar ziyartar al’ummomin da muke da tasiri don kwantar musu hankali da ba su tabbaci,” inji Kungiyar.
Daraktan Yada Labaran NEF, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, sai dai bai bayyana lokacin da za a yi zaman ba.
Amma ya bukaci Shugaba Buhari da gwamnoni cewa su yi shawara tare da lalubo hanyoyin rage tashin hankali da tabbatar da ganin duk ’yan Najeriya na zaune a kasar cikin bin doka da samun cigaba.
NEF ta jaddada muhimmancin shigarta tsakani don magance karuwar barazana gami da kalaman wasu da ake ganin sun san ya kamata, cikinsu har da zababbun shugabanni da suka yi rantsuwa don kare hakkin kowane ’yan kasa da dorewar kasar, amma suka koma haddasa tsoro da ke iya kawo rashin rikici da kuma gaba a tsakanin ’yan kasa.
Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya kuma yi zargin cewa wasu miyagu na kokarin kirkirar karya da za a yada ta bidiyo da sauran kafofin watsa labarai da niyya tunzura mutane su yi tashin hankali da juna.
A cewarsa, “Zargin da ake yi na yunkurin kisan kare dangi bai samu karbuwa ba, duk da kokarin da ake yi na matsa wa kasashen duniya don su amince cewa wasu bangarori na neman hallaka wasu.”
Ya kuma ja hankalin Shugaba Buhari da gwamnonin cewa wajibi ne su tsaya kai da fata wajen yakar masu dauke da makamai ta kowace fuksa, kuma kar a yi saken da har masu aikata laifi za su cimma burinsu.