Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya.
Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci.
Harsunan huda uku na daga cikin karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.
Ranar Arfa ita ce 9 ga watan Zul Hajji, inda alhazai ke yini a a filin Arfa domin gabatar da ibadoji.
- Gwamnatin Tinubu na amfani da talauci a matsayin makami — Atiku
- Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba
Tsayuwar Arfa ita ce babban rukunin aikin Hajji, wanda sai da shi aikin Hajji ke ciki.
A yayin tsayuwar Arfa, alhazai duka saurari huɗuba, sa’annan su yi sallolin Azahar da La’asar a hade, a matsayin Kasaru, sa’annna su bar filin Arfa kafin faduwar rana su nufi filin Muzdalifa, inda za su kwana, su wayi garin ranar Babbar Sallah a can.