Wata hajiyar Najeriya daga Jihar Filato ta rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Hajiya Jamila Muhammad ta rasu ne a yayin da alhazai ke shirin fara gudanar da aikin Hajji gadan-gadan.
Sakataren Hukumar Kin Dadin Alhazai ta Jirage Filato, Daiyabu Dauda, ya sanar a ranar Litinin cewa Hajiya Jamila ta rasu ne a asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah, sakamakon tashin cutar suga.
Ya ce Amirul Hajj na jihar da wasu manyan jami’ai sun halarci jana’izar marigayiyar, kamar yadda Musulunci ta tanada.
- Yadda magidanci ya kuɓuta bayan wata 7 a hannun ’yan bindiga
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa
- Hajji ta bayan fage: Saudiyya ta hana mahajjata 269,000 shiga Makka
Da rayuwarta, yawan alhazan Najeriya da suka rasu a aikin Hajjin bana ya ƙaru zuwa mutum uku.
Kafin ita, Najeriya ta rsa alhazai biyu da suka hada da Hajiya Adizatu Dazumi daga Jihar Edo da kuma Alhaji Saleh Saleh daga Jihar Abiya.