Gwamnatin Najeriya ta ba wa ƙasar Habasha kyautar itatuwan cashew guda 2,000 da kuma irin cashew guda 100,000.
Najeriya ta bayar da kyautar irin ne a wani bangare na yunƙurin taimaka wa ƙasashen biyu wajen samar da abinci mai yawa da kuma ƙarfafa dangantakarsu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayar da wannan kyauta, da za ta iya shuke ƙasa mai fadin hekta 600.
Shettima ya bayar kyautar ce a lokacin da ya isa birnin Adis Ababa, babban birnin kasar, domin halartar Babban Taron Majalisar Xinkin Duniya Kan Tsarin Abinci.
- Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir
- Matsalar Lantarki: Ga tsada ga rashin wuta
- An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
Ministan Harkokin Noma na Habasha, Dakta Efa Muleta Boru, ya karbi kyautar, a matsayin wani bangare na shirin ƙasashen biyu na taimakon juna a fannin noma.
A watan Yuni na 2025, kasar Habasha ta ba wa Najeriya itatuwan avocado da na kofi.
Wannan kokari yana goyon bayan shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta noma a Najeriya.
Haka kuma yana nuna cewa Najeriya na son amfani da “Diflomasiyyar Juyin Juya Halin Kore” don gina kyakkyawar dangantaka da sauran kasashe tare da magance matsalolin samar da abinci.
Mataimakin Shugaban Kasa zai gana da sauran shugabannin duniya a taron domin tattauna yadda za a inganta samar da abinci a duniya. Zai kuma halarci wasu tarurrukan don musayar ra’ayoyi da kulla kawance.