Tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya ce ba da yawan kuri’u kadai ’yan siyasa suke cin zabe ba.
Alhassan Doguwa, ya fadi haka ne a lokacin da yake magana kan takaddamar da dabaibaye shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano, wadda kotu ta kwace kujerar Gwamnan Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ta ba wa Nasiru Gawuna na APC.
A lokacin hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, Alhassan Doguwa ya bayyana cewa ko da an jefa wa dan takara kuri’u mafiya yawa a zabe, wajibi ne sai ya cika wasu sharuda da doka ta tanada.
Ya ce yin nasara a zabe ya ta’allaka ne a kan dokoki, wadanda bin su wajen yin takara da kuma gudanar da zabe ne ke ba wa zaben sahihanci da karbuwa.
- Dan sandan ya harbi mutane a cikin Keke NAPEP a Kaduna
- Kwastam sun kama albarusai 975 da aka boye a shinkafar kasar waje
Alhassan Doguwa ya ce, “Abin da mutane ba su fahimta ba shi ne harkar zabe abu ne da ya dogara kacokam a kan doka, ba batun ni na fi yawan kuri’a ba.
“Za ka iya yin nasara ta hakan ne didan ta kasance a wajen yin takara ka bi dokokin zabe da kundin tsarin mulki; wadanda wajibi ne ka cika su kafin lashe zabenka ya zama sahihi kuma karbabbe.
“Sahihin zabe ba batun yawan kuri’u ba ne kawai, domin tana iya kasancewa a cikin kuri’in da aka jefa akwai haramtattu.
“Saboda haka dole ne kafin ta tabbata mutum ya ci zabe ya zama ya cika ka’idodin da doka ta tana,” in ji Alhassan Doguwa
Ya ci gaba da cewa “A wurina abin da ke faruwa a Kano ba sabo ba ne, domin Kano ta saba kuma ta kware a harkar siyasa.
“Shi abu irin wannan, ’yan siyasarmu sun saba mayar da hankali kan abubuwa masu daure kai da ke cikinsa, kuma kuma na da ’yancin bin ra’ayinsa.”