✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam sun kama albarusai 975 da aka boye a shinkafar kasar waje

Jami'an Kwastam sun kama albarusai 975 da aka boye cikin buhanan shinkafa da aka yi fasa-kwauri zuwa Najeriya daga kasar waje.

Jami’an Kwastam sun kama albarusai 975 da aka boye cikin buhanan shinkafa da aka yi fasa-kwauri zuwa Najeriya daga kasar waje.

Jami’an da ke aiki a Jihar Ogun ne suka kama wadannan albarusai a huhunan shinkafa biyar kan hanyar Palace/Ayetoro a Karamar Hukumar Imeko Afon.

Kwanturolan Kwastam na yankin, Ahmadu Shuaibu, ya ce sun kama makaman ne bayan masu fasa-kwaurinsu sun yi kokarin wucewa da su ta barauniyar hanya.

Ya kara da cewa bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu fasa-kwaurin makamai zuwa Najeriya ne a ranar Litinin suka kama albarusan.

A cewarsa, ana ci gaba da bincike domin kamo masu hannu wajen fasa-kwaurin makaman domin su fuskanci hukunci.

Jami’in ya bayyana fasa-kwaurin makamai a matsayin babban hadari da ke taimaka wa ayyukan ta’addanci da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.