✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mafarauta 18 a musayar wuta a Taraba

Mafarauta 18 sun rasu a musayar da ’yan bindiga kusan 200 a kusa da garin Maihula na Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba

Mafarauta 18 sun rasu a musayar wuta da ’yan bindiga a kusa da garin Maihula a Karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba.

’Yan bindiga kimanin 200 sun yi kokarin kutsawa garin Bali, hedikwatar karamar hukumar, amma mafarauta suka hana su a ranar Talata.

Basaraken yankin, Kur Bali, Mahamud Abubakar, ya shaida mana cewa mafarauta sun yin nasarar dakile harin da ’yan bindiga suka kawo wa yankinsa.

Shaidu sun ce maharan da ke dauke da muggan makamai sun kashe 15 daga cikin mafarautan, suka jikkata wasu da dama.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban kungiyar  mafarauta a karama hukumar, Adamu Dantala, ya ce ’yan bindigar sun yi wa wasu mutanensa kwanton bauna a kusa da garin Dakka, suka kashe mafarauta uku.

Ya roki, “gwamnati ta samar mana da makamai da tallafin kula da iyalan wadanda suka rasu da kuma jinyar wadanda suka jikkata.”

Kakakin ’yan sanda jihar Taraba, SP Usman Abdullah bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da wakilinmu ya tura masa na neman bayani kan lamarin ba.