Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu ɗalibai biyu na Jami’ar Tarayya ta Wukari a Jihar Taraba.
‘Yan bindigar sun kai harin a wani dakin kwanan ɗalibai da ke wajen makarantar a kan titin Wukari zuwa Zaki Biam da misalin karfe 10:30 na daren Litinin inda suka yi awon gaba da ɗalibai biyu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ’yan ta’addar sun sace wani ɗalibi da wata ɗaliba da ke sashen nazarin halittu da tattalin arziki na jami’ar.
Bayanai sun ce harin ya ƙara jefa fargaba a tsakanin ɗaliban da ke zaune a wajen makaranta.
- Abin da ke faruwa a tsakanin Amal Umar da ’yan sanda
- Rikicin Kabilanci Ya Yi Ajalin Mutum 2 A Binuwai
Jami’ar hulda da jama’a ta Jami’ar, Misis Adore Awudu ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce, an yi awon gaba da wata ɗaliba da wani ɗalibi da ke zaune a wani gida da ke wajen jami’a.
Ta bayyana cewa, “tuni, jami’an tsaro da zaratan samari suka bazama domin bin sawun masu garkuwa da mutanen a daji, kuma ana sa ran suna kokarin kuɓutar da ɗaliban da aka sace.”
Ana iya tuna cewa, a kwanan baya ne yayin wani taron manema labarai, Shugabar Jami’ar, Farfesa Jude Sammani Rabo ta koka kan rashin isassun ɗakunan ɗalibai a jami’ar.
Farfesa Sammani ta ce rashin isassun ɗakunan ɗaliban na jefa rayuwar ɗaliban jami’ar da ke zaune a waje cikin haɗari.
Aminiya ta tuntubi Kwamishinan ’yan sandan Jihar Taraba, David lloyanomon, sai dai bai amsa kira ba amma ya aiko da sakon kar ta kwana.
Ya yi martani da cewa, “ina buƙatar lokaci domin tabbatar da ɗalibai ne ko akasin haka.”