✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar mutumin da aka sace tare da Hakimin Kaduna

Mako biyu ke nan da aka sace Hakimin Kujama tare da wasu mutum biyu a kusa da makarantar Bethel Baptist

An tsinci gawar daya daga cikin mutanen da aka sace su tare da Hakimin Kujama a Karamar Hukumar Chikun ta jIhar Kaduna a cikin jeji.

Aminiya ta samu bayani cewa an tsinci gawar mutumin ne a kauyen Tsohon Gayan a kan titin Kaduna-Abuja.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa ’yan bindigar ne suka kira suka fadi inda za a je a dauki gawar mutumin, shi ne jami’an tsaro da ’yan uwansa suka je inda aka fada masu suka dauko gawar.

Har yanzu dai rundunar ’yan sandan jihar ba ta ce komai ba dangane da lamarin.

Kokarinmu na jin ta bakin kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ya ci tura domin layin wayarsa ya ki shiga sannan bai amsa sakon tes da aka aika masa ba a kan batun.

Kawo yanzu Hakimin Kujama a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, ya kwashe makonmi biyu a hannun ’yan bindigan da suka yi garkuwa da shi a cikin daji.

Aminiya ta ruwaito cewa an sace  hakimin, mai suna Steven Ibrahim tare da wasu mutum biyu ne jim kaɗan bayan fitowarsu daga wani hotel da ke kusa da Makarantar Bethel Baptist a kan hanyar Kaduna Kachia makonmi biyu da suka wuce.

Makarantar Bethel ita ce inda ’yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai masu yawan gaske, sai da jibin goshi suka sako su.

Bayanai sun nuna cewa masu garkuwa da hakimin sun tuntubi iyalansa domin neman kudin fansa.