✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Sanda Sun kama Mutane 7 Kan Satar Daliban Jami’ar Wukari

An sace ɗaliban biyu — mace da namiji — a wani ɗakin kwanan ɗalibai da ke wajen jami’ar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Taraba, David lloyanomon ya bayyana cewa an kama wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a satar ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Wukari.

Kwamishinan ya ce an kama mutanen da ake zargin ne a cikin daji.

Ya ce, ana sa ran binciken da aka fara zai bankaɗo wurin da aka ɓoye ɗaliban da aka sace.

Ya shaida wa Aminiya a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro na daji suna ci gaba da  ƙoƙarin ceto ɗaliban da aka sace.

Jami’ar hulda da jama’a na Jami’ar Mrs Adore Awudu ta ce Joshua Sardauna daga sashin tattalin arziki da kuma Obianu Elizabeth Chiwuadu daga sashen nazarin halittu ne ɗaliban da aka sace.

Aminiya ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace ɗaliban biyu na Jami’ar Tarayya ta Wukari da ke Jihar Taraba.

‘Yan bindigar sun kai hari ne a wani dakin kwanan ɗalibai da ke wajen makarantar a kan titin Wukari zuwa Zaki Biam da misalin karfe 10:30 na daren Litinin inda suka yi awon gaba da ɗalibai biyu.

Ana iya tuna cewa, a kwanan baya ne yayin wani taron manema labarai, Shugabar Jami’ar, Farfesa Jude Sammani Rabo ta koka kan rashin isassun ɗakunan ɗalibai a jami’ar.

Farfesa Sammani ta ce rashin isassun ɗakunan ɗaliban na jefa rayuwar ɗaliban jami’ar da ke zaune a waje cikin haɗari.