Rahotanni sun bayyana cewa wasu fasinjojin wata babbar mota sun kashe jami’in Hukumar Kwastam a ƙaramar hukumar Kaita ta Jihar Katsina.
Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne da safiyar Laraba a ƙauyen Gamjin Makaho da ke kan hanyar Katsina zuwa Dankama.
Wasu majiyoyi sun ce motar tana jigilar fasinjojin ne zuwa garin Dankama yayin da jami’an kwastam din suka yi ƙoƙarin tsayar da ita, amma direban ya ƙi tsayawa.
An ce ana zargin ɗaya daga cikin jami’an kwastam ɗin ɗauke bindiga ya harbi wani daga cikin fasinjojin a ƙugu.
Daga ƙarshe direban babbar motar ya tsaya, inda kuma fasinjojin suka sauka domin fuskantar jami’an kwastam ɗin, kuma suka yi ta harbi.
Rahotanni sun bayyana cewa, a ƙarshe fasinjojin sun kashe jami’in kwastam ɗin wanda ba a iya tantance sunansa da matsayinsa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Kazalika, fasinjan da aka harba mai suna Bashir Na-Buzuwa, an ce shi ma ya mutu.
Marigayi Na-Buzuwa, wanda aka ce yana da kimanin shekara 27 ɗan asalin garin Doro ne a ƙaramar hukumar Bindawa kuma mazaunin Zanguna ne a cikin birnin Katsina.
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Kwastam a Jihar Katsina SC Tahir Balarabe, ya ce hukumar za ta fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin, inda ya ƙara da cewa suna ƙoƙarin ɗauke gawar abokin aikinsu.