✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka

Sabon birnin Dawakan na zamani zai kunshi manyan wuraren gudanar da bikin Daba, filayen tseren dawaki, makarantar horar da wasannin dawaki da sauransu.

Gwamnatin Jihar Katsina ta samu sahalewar Gwamnatin Tarayya domin gina Birnin Dawakai na farko a nahiyar Afirka.

Wannan amincewa ta biyo bayan wata ganawa ta musammam tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda — wanda Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina Dokta Kabir Ali Masanawa ya wakilta — da Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Malam Shehu Dikko da Ministar Al’adu, Yawon Bude da kuma Tattalin Arziqin Kirkire-kirkire Barista Hannatu Musa Musawa.

Gwamna Radda wanda ya bayyana cewa, gagarumin aikin Birnin Dawakan zai lakume biliyoyin Naira kuma zai kara inganta qokarin gwamnatin jihar na raya al’adun jihar tare da samar da hanyoyin tattalin arziki mai dorewa ga al’ummar jihar da arewacin Najeriya gaba daya.

Sabon birnin Dawakan na zamani zai qunshi manyan wuraren gudanar da bikin Daba, filayen tseren dawaki, makarantar horar da wasannin dawaki  da sauransu.