✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya

Maniyyatan da suka fito daga Malumfashi da Bakori, Ƙanƙara, Dandume, Ƙafur da Ɗanja sune rukunin farko da ake sa ran za su tashi zuwa ƙasar…

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta sanar cewa, za a fara jigilar maniyyatan jihar a ranar Lahadi 18 ga wannan wata na Mayu, 2025, zuwa Ƙasa Mai Tsarki.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Badaru Bello Karofi, ya shaida wa wakilinmu, cewa maniyyatan da suka fito daga Malumfashi da Bakori, Ƙanƙara, Dandume, Ƙafur da Ɗanja sune rukunin farko da ake sa ran za su tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa da ke cikin babban birnin jihar.

Tun farko sai da jagoran mahajjatan jahar, wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Joɓe ya bayyana cewar, gwamnatin jihar ta ɗauki duk wasu matakan da suka wajaba tun daga gida har zuwa Ƙasa Mai Tsarki domin ganin cewa mahajjatan jihar sun samu duk wata kulawa a hukumance don gudanar da aikin ibadar cikin jin daɗi da walwala.

Sai dai Amirul Hajjin ya ja hankalin maniyatan da su kiyaye duk wata doka, tun daga nan gida har a can Saudiyya inda suke ɗaukar hukunci mai tsanani ga wanda ya saɓa, musamman shiga da duk wani nau’in abin da zai sa maye da sauransu.