Hukumar Kwastam reshen Kano da Jigawa, ta kama nau’in ƙwayar Tiramol katan 491,000, tare da miƙa su ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC).
An ƙiyasta kuɗin magungunan da aka kama sama da Naira miliyan 150, kuma an gano su a cikin wata mota ƙirar Lexus SUV, a hanyar Gumel zuwa Maigatari da ke Jihar Jigawa.
- FCTA ta rufe hedikwatar PDP saboda rashin biyan haraji
- Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato
Kwanturolan hukumar a yankin, Dalhatu Abubakar, ya ce an yi wannan nasara ne bisa sahihan bayanan sirri, kuma yana daga cikin ƙoƙarin da suke yi tun bayan shigarsa ofis a watan Fabrairun 2025.
Abubakar, ya ce an shigo da ƙwayoyin ne cikin dare, kuma sun saɓa da dokokin da aka sarrafa su.
“Wannan ƙwaya tana lalata rayuka. Ka tambayi kanka shin wata ’yar uwarka, ɗanka, ko maƙwabcinka ba sa amfani da ita?” in ji shi.
Ya ƙara da cewa amfani da Tiramol yana haifar da ƙaruwar laifuka, taɓin hankali, da rashin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya.
Bisa ƙididdigar da Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) suka fitar, ana ƙiyasta cewa kimanin mutane miliyan uku ke amfani da miyagun ƙwayoyi a yankin Arewa maso Yamma.
A Jihar Kano kuwa, sama da mutum 670,000 ke amfani da ƙwayar Tiramol ba tare da izinin likita ba.
Ya kuma ce daga cikin masu amfani da ƙwayoyi a Najeriya huɗu mata ne, wanda hakan abin damuwa ne ganin rawar da mata ke takawa a cikin gida da al’umma.
Abubakar, ya buƙaci haɗin gwiwa daga wajen malamai, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin fararen hula, da hukumomin gwamnati don yaƙi da matsalar amfani da miyagun ƙwayoyi.
Taron ya ƙare ne da miƙa ƙwayoyin da aka kama zuwa hannun Hukumar NAFDAC domin ɗaukar matakin doka.