✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ya fice daga NNPP tun a 2023 — Shugaban jam’iyya

Shugaban ya ce Kwankwaso ba ya tare da jam'iyyar tun daga shekarar 2023.

Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dokta Agbo Gilbert Major, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ba ya tare da jam’iyyar tun watan Yunin 2023.

Ya ce Kwankwaso ya fice daga NNPP tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.

A yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin ‘Daily Politics’ na Trust TV, Dokta Major ya ce:

“Kwankwaso ya zama tarihi a jam’iyyar NNPP. Ya zo a wani lokaci, sannan ya tafi da nasa mutanen.

“Bisa tsarinmu da kuma hukuncin kotu daga Abiya da Abuja, ba ya cikin jam’iyyar tun 2023.”

Shugaban jam’iyyar ya kuma yi bayani game da sauya sheƙa da wasu ‘yan siyasa ke yi daga jam’iyyar, inda ya bayyana cewa yawancin waɗanda suka fice ba su da matsala da NNPP, sai dai da tsagin Kwankwasiyya.

Ya ce waɗanda suka fice har yanzu suna da alaƙa da jam’iyyar.

“Suna ci gaba da faɗa mana cewa ba su da matsala da NNPP, matsalarsu dai ita ce tsarin tafiyar Kwankwasiyya. Wasu na cewa ta koma tafiyar mutum ɗaya, kuma sun gaji da haka,” in ji Major.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka fice sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar NNPP, musamman a Jihar Kano, kuma ficewarsu babbar asara ce.

Amma ya ce jam’iyyar na nan da ƙarfinta – duk da ba ta tare da Kwankwasiyya.

Dokta Major ya kuma ƙi bayyana yadda dangantakar Kwankwaso ta ke da fadar shugaban ƙasa.

“Yana da ’yancin zuwa inda ya ga dama. Mu fa mun wuce wannan batun, mu yanzu muna duba gaba ne.”