✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ba za ta koma mulkin soja ba — Gowon

Tsohon shugaban ya ce dimokuraɗiyya ita ce turbar samar wa Najeriya ci gaba mai ɗorewa.

Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya ce Najeriya ba za ta sake komawa mulkin soja ba.

Ya bayyana haka ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja yayin ƙaddamar da littafi mai suna “Military Factor in Nigerian History, 1960-2018”, domin murnar cika shekaru 70 da kafa ƙungiyar Tarihi ta Najeriya (HSN).

Gowon ya ce duk da irin gudunmawar da sojoji suka bayar a tarihin Najeriya, musamman a lokacin yaƙin basasa da kuma samar da ababen more rayuwa bai kamata su sake tsoma baki a siyasa ba.

Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya, duk da kurakuran da ake samu a cikinta, ita ce hanya mafi dacewa don ci gaban ƙasa.

“Ya kamata zamanin mulkin soja ya ƙare a Najeriya. Duk da gazawar dimokuraɗiyya ita ce hanya mafi kyau wajen ci gaban ƙasa da kuma bai wa mutane dama su shiga harkokin mulki,” in ji Gowon.

Ya amince cewa a wasu lokuta a mulkin soja ya tauye ’yancin jama’a kuma ya hana dimokuraɗiyya ci gaba.

Sai dai ya ce, idan aka amince da kuskuren da aka yi a baya, za a samu ingantaccen tsarin siyasa a gaba.

“Mulkin soja ya zo da ci gaba da kuma raɗaɗi. Don mu samu ci gaba, dole ne mu karɓi gaskiya game da abin da ya faru a baya, mu gyara gaba,” in ji shi.

Gowon ya ƙara da cewa akwai buƙatar rundunar soji ta mayar da hankali wajen kare ƙasa, ta inganta fasaharta, sannan ta ƙara haɗin kai da hukumomin fararen hula domin samar da zaman lafiya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Shi ma tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya yabawa irin gudunmawar da sojoji suka bayar ta fuskar ginea hanyoyi, gadoji da wanzar da zaman lafiya.

Sai dai ya ce ba za a iya watsi da batun take hakkin ɗan adam a lokacin mulkin soja ba.

Littafin da aka ƙaddamar ya samu yabo daga masana da suka ce ya yi bayani dalla-dalla kan tasirin soja a siyasa, tattalin arziƙi da zamantakewar Najeriya.

An shawarci ɗalibai, masu tsara manufofi da jami’an tsaro da su karanta littafin domin ƙara samun ilimi.