Babbar Kotun Jihar Adamawa ta sake dage gurfanar da Kwamishinan Zabe na Kasa na Jihar (REC) da aka dakatar, Barista Hudu Ari Yunusa, zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba.
A yau Litinin 23 ga watan Oktoba ne ya kamata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gurfanar da dakataccen jami’in nata a gaban kotun, amma hakan bai yiwuwa saboda kotun ba ta samu yin zaman ba.
- Bayanan sahihancin takardun Tinubu sun yi karo da juna —Kotun Koli
- An Yi Wa Dalibar Kwalejin Ilimi Kisan Gilla A Gombe
Hudu Yunus wanda INEC ta dakatar kan takaddamar zaben Gwamnan Adamawa, yana fuskantar zargin bayyana sakamakon zabe na bogi, haddasa rikici, yin sojan gona da kuma karya rantsuwar aiki na zama dan ba-ruwanmu.
A baya dai kotu sanya 27 ga watan Yuli, 2023 domin gurfanar da Hudu Ari, amma hakan bai yiwuwa saboda rashin bayyanarsa a gaban kotu, lamarin da ya sa sau uku Mai Shari’a Benjamin Manji, yana dage zaman.