✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Yi Wa Dalibar Kwalejin Ilimi Kisan Gilla A Gombe

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wata daliba mai suna ’yar aji uku a Kwalejin Ilimi (COE) ta Jihar…

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wata daliba mai suna ’yar aji uku a Kwalejin Ilimi (COE) ta Jihar Gombe da ke garin Biliri.

Aminiya ta samu labarin cewa ’yan ta’addan sun kashe dalibar ce a safiyar ranar Lahadi a unguwar Zazzagawa inda dakunan kwanan ɗalibai da ba a cikin makaranta ba suke.

Wani makwabcin Yosi ya shaidawa wakilinmu Yosi ’yar asalin garin Baganje ce a yankin Karamar Hukumar Billiri, ta gamu da ajalin ta ne da sanyin safiyar ranar Lahadi din lokacin da wasu ’yan ta’adda suka far mata a dakin kwananta, suka kashe ta suka tsere.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da faruwar kisan dalibar inda ya ce suna gudanar da bincike dan gano wadanda suka aikata kisan gillar.

Ya ce an kai gawar dalibar dakin ajiyar gawa har zuwa lokacin kammala bincike.

Kisan gillar da aka yi wa daliba Yosi ya zo kasa da sa’o’i 48 da kisan wata mata mai ’ya’ya 8 Aishatu Abdullahi da wasu ’yan ta’adda suka kashe a gidanta unguwar Jekadafari da da ke garin Gombe, inda a ranar Lahadi ’yan Sanda suka kama wadanda ake zargin.