✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kara mafi karancin albashin ma’aikata — Tinubu

Babu matakan da suka fi wadanda muka dauka sauki.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar kara mafi karancin albashin ma’aikata.

Tinubu ya fadi haka ne a jawabin da ya yi wa ’yan Najeriya a Yammacin wannan Litinin din.

“Karin albashi na nan tafe,” a cewarsa.

“Da zarar mun daddale game da mafi karancin albashi da kuma sauran abubuwa, za mu saka shi cikin kasafin kudi domin fara aiki cikin gaggawa.

“Tuni mun kaddamar da tsarin sake duba albashin ma’aikata.”

Haka kuma a jawabin nasa, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta dauki tsauraran matakai ne saboda sun zama dole, “kuma babu waɗanda suka fi su sauki.”

“Da a ce akwai hanyoyin da suka fi su sauki da na bi,” in ji shi.

“Abin da zan iya yi kawai shi ne daukar matakan da za su saukaka yanayin.

“Gwamnatina za ta tabbatar da yin aiki tare da dukkan jihohi don rage radadin da ’yan kasa ke ji.”