A yau Alhamis za a soma biyan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya albashinsu na watan Janairu kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Akanta-Janar ta tabbatar.
Sanarwar ta ce an samu jinkirin biyan albashin ne sakamakon wata tangarda da aka samu da tsarin biyan albashin da gwamnatin ke amfani da shi.
- Za a buɗe makarantu 23 da aka rufe tsawon shekaru 10 a Oyo
- Ana zargin matashi da sace mazakutan samari 5 a Jigawa
Wannan dai na zuwa bayan da aka riƙa korafe-korafen kan jinkirin biyan albashin da aka yi a sakamakon abin da gwamnatin ta kira rashin daidaita sabon kasafin kuɗin 2024 da tsarin biyan albashin.
Ana iya tuna cewa, a ranar 31 ga watan Janairu ne Gwamnatin Tarayya a cikin wata takarda da fitar ta bai wa ma’aikata uzuri tare da ankarar da su cewa za a samu jinkirin biyan albashin watan Janairu har zuwa wani ɗan lokaci sabanin yadda aka saba.
Sai dai da yake magana da Aminiya dangane da jinkirin biyan albashin, jami’in hulɗa da al’umma na Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Bawa Mokwa, ya ce an warware duk wata tangarda saboda haka ma’aikata za su soma samun albashinsu daga yau Alhamis.
“Mun gano bakin zare kuma mun warware tangardar da muka fuskanta, saboda haka ma’aikata za su soma samun albashinsu daga Yammacin wannan Alhamis din.