✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala kwaso alhazan Najeriya daga Saudiyya

NAHCON ta kammala aikin ne da alhazan Kaduna da na Bauchi.

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta kammala kwaso alhazan Najeriya da suka sauke farali a aikin hajjin 2023.

NAHCON ta kammala aikin kwaso alhazan ne da na Kaduna mutum 298 da alhazan Jihar Bauchi guda daya da kuma jami’ai 16 a jirgin saman Azman.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Mataimakin Daraktan Yada Labarai na NAHCON, Mousa Ubandawaki, ya ce jirgin karshe na zuwa ne kwanaki hudu gabanin ainihin ranar da hukumar ta kayyade.

Ubandawaki, ya ce shugaban hukumar, Zikrullah Kunle Hassan, ya jaddada godiyarsa ga ‘yan Najeriya bisa gagarumin goyon bayan da suka bai wa hukumar yayin aikin hajjin da aka kammala.

Shugaban, yayin jawabin da ya yi wa alhazan Najeriya na karshe a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah, ya nuna godiyarsa da taimakon da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima suka bayar wajen ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2023.

Hassan, ya bayyana cewa shiga tsakani da suka yi ya bai wa hukumar damar mika kudaden ta da suka makale zuwa kasar Saudiyya sannan kuma ta lallashi Hukumar Kula da Zirga-Zirgar jiragen sama ta kasa (GACA) da ta kara ware wa kamfanonin jiragen sama na Najeriya.

“Ina so na bayyana matukar godiya ga gwamnatin Najeriya, musamman Shugaban Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa kan sa baki da goyon bayan da suka yi a kan lokaci.

“Taimakonsu ya ba da gudummawa wajen nasarar da aka samu a yau.”

Ana iya tuna cewa hukumar ta sanya 3 ga watan Agusta a matsayin ranar karshe ta kammala jigilar alhazan Najeriya.