Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar cewa ranar 15 ga watan nan na Mayu za a fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya.
Shugaban NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, ne ya sanar da haka a taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah da ke gudana a Abuja a safiyar Alhamis.
Jalal Arabi ya ce a bana maniyyata kimanin 65,500 ne za sauke farali daga Najeriya, inda za su shafe akalla kwanaki hudu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa za a y jigilar maniyyata ne daga cibiyoyi 10 a fadin Najeriya.