✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu aurar da amarya mu sayar da ’yan daukar ta 62 —’Yan bindiga

Sun ce za su aura wa dayansu amaryar idan ba a kawo kudin fansa Naira miliyan 100 ba

’Yan bindiga sun saki bidiyon amaryar da suka sace tare da ’yan daukarta 62 a a Jihar Kasina suna barazanar aurar da su da kuma sayar da su.

A cikin bidiyon ’yan bindiga sun ce za su aura wa dayansu amaryar idan idan ba a kawo kudin fansa Naira miliyan 100 ba.

Sun kuma kara da cewa za su sa sayar ya daragowar mata 62 da suka sace tare da amaryar ranar Alhamis da ta gabata a hanyarsu ta kai ta dakinta a garin Damari da ke Karamar Hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

A harin na ranar Alhamis, an kashe ’yan banga 55 sannan aka yi awon gaba da mutane 55 da ke rakiyar amaryar, ciki har da kananan yara da kawayenta daga garin Dandume, kuma har yanzu ba a sako su ba.

Motar masu daukar amaryar ta fada tarkon maharan ne a Sabuwa, daga bisani ’yan bindigar suka saki bidiyo cewa mutane 63 ne a hannunsu.

A cikin bindiyon, ’yan ta’addan sun rataya wa direban da kuma wasu daga cikin mutanen bindigogi kirar AK-47, amaryar kuma sanye da kakin sojoji, a yayin da ’yan rakiyarta suke rokon a kawo musu dauki a biya kudin fansa.

Iyalan amaryar sun tabbatar wa Aminiya cewa masu garkuwar suna neman kudin fansa miliyan N100 kafin su sako duk mutanen.

Wadanda aka sace

Wani kawun amaryar, Haruna Abdullahi, wanda ’ya’yansa guda da ’yan uwansa mata takwas na cikin wadanda aka sacen, . ya shaida mana cewa: “Masu garkuwar na neman Naira miliyan 100 kudin fansa, alhali cikinmu babu wanda ya taba ganin irin wadannan kudade; don haka na fada musu cewa ba mu da kudin da suke nema.”

A cewarsa, maharan sun shaida masa cewa sun yi bidiyon ne domin kalubalanta gwamnan jihar, Dikko Umar Radda, wanda ya lashi takobin ceto mutanen.

“Sun ce sun yi bindiyon don su nuna wa gwaman cewa da gaske suke,” in ji Haruna Abdullahi wanda ya nuna godiya ga gwamnan bisa kokarinsa ne kubutar da mutanen.

Shi ma wani dangin amaryar  mai suna Zubairu, ya ce matarsa da ’ya’yansa shida da mutum 13 daga cikin danginsa na cikin ’yan rakiyar amaryar da aka yi garkuwa da su a harin.

Karuwar garkuwa da jama’a

A baya-bayan nan dai garkuwa da jama’a ya karu a Jihar Katsina, duk da cewa abin ya lafa da awatanin da suak gabata.

Ana iya tuna cewa a lokacin da aka sace wadannan mutane wasu mahara daga Dajin Siddi sun kai hari a yankin Tashar Nadaya, da ke kusa sa garin Gazari da ke iyaka da Karamar Hukumar Sabuwa.

A harin ne mahara suka kace wani a kan babur suka dauke baburin.

Maharan sun kuma bude wa wasu mutum hudu wuta suka yi awon gaba da baburansu.

A Karamar Hukumar Batsari kuma ’yan bindiga sun sace mutane 30 a kauyen Tasharnagulle, amma daga bisano sojoji sun ceto mutanen suka mika su ga gwamnatin jihar.

‘Abin da muke yi’

Kwamishinan tsaron Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu Danmusa, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zauna da shugabannin hukumomin tsaro kan yadda za a ceto mutanen ba tare da komai ya same su ba.

Don haka ya roki danginsu da su kara hakuri, domin aikin dare daya ba ne.

A nasa bangare, kakakin ’yan sadan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce rundunar ta riga ta kaddamar da aikin ceto mutanen da kuma hukunta masu laifin.