Gwamnatin rikon kwaryar kasar Libya na karbar bakuncin wakilan kasashen duniya a wani taro kan yadda za a samar da hadin kai tsakanin ’yan kasar.
Wannan na zuwa ne gabanin babban zaben da ake shirin gudanarwa a ranar 24 ga Disamba, 2021 a kasar.
- Najeriya A Yau: Harin Jirgin Kasa ya ja wa Najeriya asarar N25m a kullum
- Kar sojoji su kuskura a hana zaben gwamnan Anambra —Buhari
Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin rikon kwaryar Libya suna kokarin ganin an samu goyon bayan ilahirin bangarorin siyasa a kasar don ganin cewa an yi zaben shugaban kasa da na ’yan majalisa a ranar 24 ga watan Disamba cikin nasara.
Wasu daga cikin kasashen duniya sun soma nuna goyon baya ga yunkurin sake dawo da mulkin farar hula a Libya, bayan kifar da gwamnatin Shugaba Muammar Gaddafi shekara 10 da suka wuce.
Tuni kasar Faransa ta sake bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli na kasar, wanda aka rufe shi shekara bakwai da suka gabata saboda tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan boren da aka yi wa gwamnatin Gaddafi.