✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kotu ta yanke wa wanda ya kona mutane a cikin masallaci hukuncin rataya a Kano

Baya ga hukuncin kisa, alkali ya ba da umarnin a yi masa bulala 150, a kwace babur dinsa a sayar a gyra masallaci da kudin…

Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu.

An samu Shafi’u da laifuka hudu, ciki har da kisan kai da kuma barna ta hanyar gobara. Baya ga hukuncin kisa, alkali ya ba da umarnin a yi masa bulala 150, tare da biya tarar N1,500, sannan kuma a kwace babur dinsa mai kafa uku, inda za a sayar, a yi amfani da kudin da aka samu wajen gyaran masallacin da ya lalace.

Yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu bakwai, ciki har da hakimin kauye da kuma wani jami’in ’yan sanda.

Daya daga cikin shaidun, wanda dan uwan Shafi’u ne, ya bayyana cewa wanda ake tuhumar yana da tarihin kokarin cutar da ’yan uwa, kuma an bayyana shi a matsayin mai cikakken hankali bayan binciken tabin hankali.

Wani shaida kuma ya bayyana yadda ya tsira a lokacin da masallacin da ke ci da wuta tare da munanan raunuka kuma ya ga Shafi’u yana gudu.

Shafiu ya shaida wa kotun cewa ya sayi man fetur a ranar 14 ga Mayu, 2024, don yayyafa wa masallacin sannan ya cinna masa wuta, ya rufe kofofinsa kuma ya samu konewa a lokacin da yake aikata laifin. Furucinsa, tare da konewar da ke bayyane a hannayensa yayin bayyanarsa a kotu, sun tabbatar da shari’ar masu gabatar da kara.

Daraktan gabatar da kara na Jihar Kano ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin, inda ya bayyana cewa ya nuna girman laifin.

Sai dai lauyan Shafi’u ya nuna yiwuwar daukaka kara tare da nuna damuwa game da yanayin da yake tsare.

An ruwaito cewa lamarin ya samo asali ne daga rikicin gado, inda Shafi’u ya yi niyyar kai hari ga ’yan uwansa da ya yi imanin sun zalunce shi.