✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa ta haramta shan sigari a cikin jama’a

Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a.

Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a.

Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani.

Ministar Lafiya da Iyali na kasar, Catherine Vautrin ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce, “Dole a daina shan sigari a wuraren da yara suke.

“’Yancin shan sigari ya kare ne a inda ’yancin yara na shakar tsaftatacciyar iska ya fara,” kamar yadda ministar ta shaida wa jaridar Ouest-France ta kasar.

Kazalika, dokar za ta hana dalibai shan sigari a gaban makarantu, kuma duk wanda aka samu ya karyata zai iya fuskantar hukuncin biyan tarar da ta kai Dala 154, kusan Naira 250,000 ke nan.

A cewar alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), fiye da kaso 35 cikin 100 na mutanen kasar Faransa na ta’ammali da sigari.