Ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dawo gida nan take domin tunkarar matsalar rashin tsaro da ke ƙara ƙamari.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a jihohin Filato, Zamfara, Borno da wasu sassan ƙasar.
Shugaba Tinubu ya tafi Faransa a ranar 2 ga Afrilu don “tafiyar aiki” na makonni biyu. Daniel Bwala, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Manufofi, ya ce tafiyar na da nufin yin yin bitar tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da kuma sauye-sauyen, gabanin cikar shekaru biyu na gwamnatin.
A cikin saƙonsa na ranar Laraba, Obi ya ce ya zama dole ya ja hankalin “shugabanmu mai janyewa, zuwa ga ƙalubalen tsaro a gida,” yana mai jaddada buƙatar “ya dakatar da kansa bayan da yake yi a ƙasar waje nan take, ya dawo gida domin magance matsalar tsaro da ta mamaye ƙasar.”
- An kashe shanu 36, an ba 42 guba a Filato
- Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda
Ya bayyana cewa, wannan kira nasa na gaggawa ya zama dole saboda ƙaruwar ta’addanci da miyagun laifuka a faɗin Najeriya, tare da rashin ganin matakan da gwamnati ke ɗauka a zahiri.
Ya bayyana wa Tinubu cewa, “A cikin makonni biyu da kuka yi a waje, sama da ’yan Najeriya 150 sun rasa rayukansu sakamakon rashin tsaro a faɗin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Zamfara. Fashewar bututun mai da aka yi a yankin Neja Delta, ya ƙara nuna kasar cikin kunci.
“A Arewa Maso Gabas, shugabannin Jihar Borno na kuka game da dawowar ’yan ta’adda, inda ake kashe sojoji da fararen hula ba tare da dalili ba. A Kudu Maso Gabas, labarin haka yake: kashe-kashe da garkuwa da mutane.
“A cikin duk waɗannan, shugaban kamfanin da ke da cikin matsala, mai suna Najeriya, ya bar hedikwatar kamfanin ya je ya yi zamansa a ƙasar Faransa,” in ji Obi.
Ya jaddada cewa, babban aikin kowace gwamnati shi ne tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan kasarta, yana mai tambayar “dalilin zaman a wata ƙasa da shugabanninsu suka tabbatar da zaman lafiya yayin da jini ke ci gaba da zuba a tamu ƙasar.”
Obi ya ce, gwagwarmayar samun Najeriya ta gari ba batu ne na tabbatar da cewa kowane ɗan kasa ya ga, ya ji, kuma ya amfana da manufofi da shawarwarin waɗanda ke kan mulki.
“Don haka, ina kira ga shugaban ƙasa da ya dakatar da duk abin da yake yi a Faransa da sauri ya dawo gida ya ɗauki mataki ta hanyar magance waɗannan batutuwa masu tayar da hankali,” in ji Obi.