✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makwabta sun kai karar ma’aurata saboda carar zakaransu

A wannan shekarar ce alkali zai yanke hukunci kan wannan batu na shari’ar carar Zakara Ricco.

Wasu magidanta da suka mallaki wani zakara (Ricco) jinsin Bantam daga Bourgoin-Jallieu a sashen Isère na kasar Faransa, sun karɓi sammaci domin bayyana a gaban kotu sakamakon korafin da wani makwabcinsu ya yi game da carar zakaran.

Korafin da suka yi ya hada da, rashin barci saboda karar da zakaran yake yi a yayin carar, kamar yadda mai gabatar da ƙara ya ambata, wanda ya gayyaci masu zakara (Ricco) zuwa kotu a watan Janairun 2025.

Mutumin, wanda ya fi son a sakaya sunansa, yana daya daga cikin makwabtan masu ikirarin cewa, carar zakaran ba za a iya jure ta ba da daddare da rana.

Masu wannan zakaran mai shekaru 5 a koyaushe suna musanta wadannan ikirari, inda suka kafe a kan cewa, zakaran yana da tsarin sarrafa kansa wanda ya tsara yin carar daga karfe 8:30 na safe a lokacin hunturu da karfe 9:00 na safe a lokacin rani.

Sun dage cewa, zakara ya kan yi cara kamar sau 15 a cikin mintuna 15 da safe, sannan sai ya kara yin cara da rana.

“Akwai tsarin da yake bi, wanda yake nuna cewa, yana rufe yin carar daga karfe 8 na dare. Kuma yana farawa da karfe 9 na safe a lokacin rani, 8:30 na safe a cikin hunturu,” in ji Franck, mamallakin zakaran (Ricco).

Da muka kawo zakarar, sai muka cewa kanmu don kada ya damu makwabtanmu, sai muka tabbatar an bude kofar kejinsa daga karfe 8:30. Sai muka yanke shawarar buɗe shi da karfe 9:00 na safe.

“Mun fahimci cewa, lokacin sanyi, kaji ba sa yin kwai don suna bukatar haske.

“Don haka a lokacin sanyi, muna bude shi da karfe 8:30, kuma a lokacin rani muna bude shi daga karfe 9:00 na safe.”

Ma’auratan sun koma garin Bourgoin-Jallieu da ke birnin shekaru 25 da suka gabata don yin rayuwa mai sauki kuma, inda suka yi mamakin matakin shari’a da makwabcinsu ya dauka.

Da farko sun yi kokarin sasantawa ta hanyar tattaunawa da makwabtan, amma hakan bai yuwu ba, kuma makwabcin ma’auratan ya yanke shawarar kai su kotu.

Franck ya yi ikirarin cewa, ya yi magana da kowanne daga cikin makwabtansu, kuma babu dayansu da ke da matsala da carar zakaran.

“Mun je wajen dukkan makwabtan, mun san wasu daga cikin matsalolinsu saboda mun zauna a nan tsawon shekaru 25,” in ji Franck.

“Mun tambaye su ko zakara yana damun su. Duk wadanda muka tuntuba cewa zakara ya dame su. Sai a samu akasin haka, suna son su ji carar zakara.”

A gefe guda, wacce ta shigar da karar, wanda ta koma Bourgoin Jallieu a cikin 2021, ta kafe a kan cewa carar da zakaran ke yi tana hana ta jin dadin lambunta da yin barci mai kyau, kuma suna son yanayin ya canza.

Rikicin shari’ar game da carar zakarar ya mayar da hankali ne kan dokar Faransa ta Janairu 29, 2021.

A gefe guda, masu zakaran sun yi imanin cewa, suna zaune a cikin yankin da ya kasance yankunan karkara ce, yayin da makwabcinsu ya yi imanin cewa, gundumar Boussieu ba ta kasance a cikin karkara ba.

A wannan shekarar ce alkali zai yanke hukunci kan wannan batu. Abin farin ciki ga zakara Ricco, yana da goyon bayan shafukan sada zumunta na zamani.

An kirkiro masa wani shafi a Fesbuk na goyon bayansa, inda mutane ke karfafa masa gwiwa ya ci gaba da yin cara da kuma gayyatar masu sukar zakaran da su yi kaura idan ba sa son “cararsa”