Kotu ta yanke wa wani magidanci mai shekara 56 hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan laifin yin fyaɗe ga agolarsa ’yar shekara 14.
Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa mutumin hukuncin ne byan an gurfanar da shi kan zargin aikata laifin a watan Oktoban shekarar 2024, watanni bakwai da suka gabata.
A yayin zaman kotun da ke zamanta a garin Ado-Ekiti, mai gabatar da ƙara, Julius Ajibare ya gabatar da shaidu shida da ke tabbatar da laifin da ake tuhumar mijin mahaifiyar yarinyar da yi mata fyaɗe.
Kazalika ya gabatar da wasu hujjoji da kuma sakamakon gwajin asibiti da suka tabbatar da laifin da ake zargin magidancin da aikatawa.
- Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano
- NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su
Bisa haka ne kotun ta yanke wa mutumin hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan ta saurari jawabansa ta bakin lauyansa, Olajide Adedeji, wanda ya gabatar da shaida guda ɗaya.