Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 3 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan shari’ar BBC da mawaƙi Abdul Kamal.
Tunda farko Abdul, ya maka kafar ne a kotu, inda yake neman ta biya shi diyyar Naira miliyan 120, kan zargin amfani da waƙarsa a shirinsu na “Daga bakin mai ita” ba tare da izininsa ba.
- Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano
- Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum
A zaman shari’ar na ranar Litinin, lauyan mai ƙara, Barista Bashir Ibrahim Umar, ya gabatar da makaɗin waƙar, Muhammad Sani Uba a matsayin ɗaya daga cikin shaidun wanda ke ƙara.
Makaɗin ya tabbatar wa kotu cewa shi ne, ya yi wa Kamal kiɗan da ake shari’ar a kansa.
Daga bisani alƙalin kotun, ya sanya ranar 3 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan shari’ar.