A wannan Larabar Shugaban Kasa Bola Tinubu zai tafi ziyarar aiki ta makonni biyu a ƙasar Faransa.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce a yayin ziyarar shugaban ƙasar zai yi bitar ayyuka da nasarorin gwamnatinsa yayin da ta ke gab da cika rabin zango.
Haka kuma zai duba duba garanbawul ɗin da ya yi da gaggauta ci gaban da ya ke so a samu a shekara da ke tafe.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta samu nasara a fannin tattalin arziki, inda sanarwar ta bayar da misali da bunƙasar asusun ajiyar kuɗaɗen waje da babban bankin ƙasar ya ce ya kai $23.11 biliyan — idan aka kwatanta da $3.99 biliyan da suka ce sun tarar a shekarar 2023.
Shugaban ya bayyyana cewa zai ci gaba da jagorantar al’amuran gwamnatin Nijeriya, a yayin da yake Paris gabanin dawowarsa nan da makonni biyu.