Daliget sun tayar da jijiyoyin a wurin taron haɗakar siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi domin fafatawa da shuagaban kasa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Ana tsaka da taron Kungiyar Tuntubar Siyasa ta Kasa Reshen Arewa a Abuja ne hayaniya ta kaure bayan tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya sanar da wanda suna daliget da zai wakilci Jihar Jigawa.
Rashin gamsuwar sauran daliget din jihar dadi ba suka tayar da jijiyoyin wuya, inda suka hau kan mumbari suka dauke wanada aka ayyanan suka hana shi magana da yawunsu.
Daba bisani an yi nasarar shawo kan rikicin, inda aka zabi dan tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, Mustapha Lamido, da wani daliget kuma suka gabatar da jawabi a madadin wakilan jihar.
- Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato
- Ko gwamnoni duka za su koma APC ba zai hana mu kayar da Tinubu a 2027 ba — Babachir
- An kashe matashi yayin rikici a ƙauyukan Kano
Atiku wanda ya dade yana neman takarar shugaban kasa a Najeriya yana kokarin jagorantar jam’iyyun adawa domin kayar da Tinubu a zaben na 2027, yana daga cikin fitattun ‘yan siyasar da suka shiga hadakar APC a gabanin zaben 2015.
Hadakar tasu ta kai ga dan takarar APC Muhammadu Buhari, ya yi nasarar kayar da shugaban kasa Goodluck Jonathan a lokacin. Daga bisani ya fice daga APC zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, inda yake hankoron cika burinsa na zama shugaban kasa.
Yadda Atiku da Obi suka tattauna da gammayyan ’yan siyasara Arewa
Daga cikin wadanda ke cikin hadakar tasu Atiku har da dan takarar mataimakin shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Datti Baba-Ahmed da tsoffin ministoci a zamanin Buhari irin su kamar Rotimi Amaechi (Sufuri) da Abubakar Malami (Shari’a) da Bolaji Abdullahi (Wasanni).
Sauran tsoffin kusoshin APC da suka shiga hadakar sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban APC na Kasa (Arewa) Salihu Lukmanda da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a zamanin Buhari Babachir David Lawal.
Sauran sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Kyaftin Idris Wada, da tsohon Shugaban Kwamitin Aminitattu na PDP, kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Adolphus Wabara, da sauransu.
Duk da cewa wasu mahalarta taron sun bayyana cewa manufarsu ita ce lalubo mafita ga matsalolin da ke ci wa yankin Arewa tuwo a kwarya, amma manazarta sun bayyana cewa babban makasudin taron shi ne tattuna yadda ’yan adawar za su kayar da Tinubu a zaben 2027.