Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya rubuta wasiƙa ga kwamitin tsaro na majalisar, inda ya nemi ’yan kwamitin su taimaka don kauce wa mummunar annoba a Gaza.
“Yayin da ake fuskantar shiga bala’in rasa agaji a Gaza, ina neman Kwamatin ya taimaka wajen kauce wa aukuwar bala’i, kuma ya nemi a tsagaita wuta don kai agaji,” in ji Guterres a cikin wani saƙo da ya walafa ranar Laraba.
Cikin wasiƙar da ya rubuta, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba daga baya da kuma tsaron yankin.
Ya ƙara jaddada buƙatar tsagaita wuta saboda yadda lamarin ke ƙara ƙazancewa a Gaza, da kuma neman zaman lafiya a yankin.
- Tudun Biri: An fara tattauna biyan diyyar Harin Mauludi
- Hukumar Shari’a ta dakatar da alkali kan yanke hukunci ta hanyar da ba ta dace ba
Guterres yace “wannan ne karon farko da nake ɗaukar irin wannan mataki tun bayan zama na sakatare janar na MDD a 2017”.
Bugu da kari, Guterres ya ce alhakin ƙasashen duniya ne su shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin.
Ya yi amfani da ayar doka ta 99 ta MDD, wadda ta ba shi damar jawo hankalin Kwamatin Tsaro kan “duk wani batu da yake ganin zai iya barazana ga zaman lafiyar duniya da tsaro”.
Guterres wanda ke kira da a “tsagaita wuta cikin gaggawa” tun daga ranar 18 ga Oktoba – ya kuma bayyana “mummunan wahalar dan Adam, lalacewar jiki da kuma raunin gaba daya a duk fadin Isra’ila da yankunan Falasdinawa da ta mamaye.”
A yayin da ake ci gaba da kai hare-haren, Mista Guterres ya ce ya yi imanin lamarin “na iya kara tsananta barazanar da ake fuskanta na wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.”
Ya yi gargadin cewa zaman lafiyar jama’a a Gaza na iya wargaje wanan ba da jimawa ba a daidai lokacin da tsarin ayyukan jin kai ke durkushewa.
“Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa zuwa wani bala’i wanda zai iya haifar da tasiri ga Falasdinawa gaba daya da kuma zaman lafiya da tsaro a yankin.”
“Ina tsammanin zaman lafiyar jama’a zai wargaje nan ba da jimawa ba saboda hali mai tsanani da ake ciki, wanda hakan zai sa ko da taimakon jin kai ba zai yiwu ba,” in ji shi.
Haka kuma, ya yi nuni da cewa, sama da mutane 1,200 a Isra’ila ’yan Hamas sun kashe suka a ranar 7 ga Oktoba, ciki har da yara 33, da kuma mutane 130 da har yanzu ake tsare da su.
“Dole ne a sake su ba tare da wani sharadi ba. Batun cin zarafin jima’i a lokacin wadannan hare-haren yana da ban tsoro,” in ji shi.
Ya jaddada cewa idan aka tsagaita wuta, akwai fatan zaman lafiya da kuma damar kai agajin taimako.
Amma duk da haka, jakadan Isra’ila na Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan bai amince da kiran da Mista Guterres ya yi kan mataki na ayar doka ta 99 ta MDD ba.