✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tudun Biri: An fara tattauna biyan diyyar Harin Mauludi

Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna sun fara tattaunawa kan biyan diyyar masu Mauludin da jirgin soji ya kashe a kauyen Tudun Biri

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce sun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan yadda za a biya diyya ga mutanen da harin jirgin soji a taron Mauludi kauyen Tudun Biri ya shafa.

Uba Sani, yi alkawari a ranar Alhamis na tabbatar da ganin cewa an biya su diyya tare da tallafa wa wadanda abin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ziyarci wadanda harin bom din ya shafa da suke kwance a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko inda yajajanta musu.

Shettima ya bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sha alwashin hukunta duk masu hannun a harin bon din da jirgin sojin ya kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 100.

Mataimakin shugaban kasan ya cen nan ba da dadewa ba,  Tinubu zai karbi sakamakon binciken kwamitin da ya kafa domin gano musabbabin harin jirgin sojin a Tudun Biri.

Daga nan, ya mika wa gwamnatin jihar gudunmuwar miliyan 20 daga aljihun shugaban kasa, ga wadanda harin Mauludin na Tudun Biri ya shafa, sannan shi ma ya ba da miliyan 10.

Shi ma Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen ya ba su tallafin miliyan 10 daga aljihunsa, ya kuma yi alkawarin gina makaranta da asibiti a garin na Tudun Biri.

Tinunu na da kyakkyawar manufa ga Arewa —Shettima

A jawabin mataimakin shugaban kasan, ya rantse da cewa Shugaba Tinubu yana da manufa kyakkyawa ga yankin Arewacin Najeriya na da ma kasar baki daya.

Shettima ya ce “Wallahi [Tinubu] yana da kyakkyawar niya ga al’ummar Arewa duk da maganganu da wasu ke yi .

“A lokacin da wannan abin ya faru ya kira ni kusan sau 17 saboda a lokacin yana Dubai wurin taro domin yana son ya ga an kawo tallafi ga mutanen da abin ya shafa.”

Ya bayyana cewa Gwamnatin Tinubu za ta gina gidaje guda 1,000 a Jihar Kaduna, a karkashin shirinta na Fulako da nufin magance matsalar tsaro.

Ya ce gidaje 500 a za a gina su ne Kudancin jihar, sauran 500 kuma a Arewacin jihar a karkashin shirin na Yaki da Ta’adanci, wanda kuma kowa da kowa ne za su amfana da gidajen.

Shettima ya bayyana cewa shirin Fulako da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Arewa Maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Ya lisssafo jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Katsina da Kaduna da Binuwe da Neja a matsayin wadanda da za su amfana.