Alhaji Nastura Ashiru Sherif Wanda shi ne Mai Magana da yawun Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG), ya bayyana matsalar tsaro da yankin ke fama da shi a matsayin wata fitina.
Ya ce akwai bukatar kowane mahaluki a yankin na Arewa ya bayar da gudummuwa wajen magance wannan fitina da ke addabar su.
Nastura Ashiru Sherif ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kaɗan bayan ganawarsu da gwamnonin Arewa a taron da gwamnonin suka gudanar a Kaduna a ranar Talata.
Ashiru Sherif ya ce sun gabatar da kuduri a gaban gwamnonin na matakan da ya kamata a dauka domin shawo kan matsalar tsaro da garkuwa da mutane da ke addabar yankin.
- An kama barawon wayan da ya caka wa budurwa wuka a Yobe
- An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano
“Ba wai amfani da ƙarfin soja kaɗai ba ne matakin yaƙi da matsalar tsaro, akwai bukatar yaƙi da talauci da samar da ayyukan yi ga matasa wanda hakan babban mataki ne na kawar da matsalar,” in ji shi.
Gamayyar Kungiyoyin sun ce da akwai shiri da suke da shi inda za su sanya dukkanin jama’ar yankin ciki domin lalubo hanyoyin dakile matsalar tsaro tun daga kan gwamnoni da sarakuna da malamai zuwa ’yan jarida da masu wasannin kwaikwayo.
Sherif ya ce sun gamsu da irin salon da gwamnoni ke ɗauka a yanzu ta hanyar tunkarar matsalar domin ko a ganawar da suka yi da su sun ga yadda gwamnonin suka nuna damuwa kan halin da yankin Arewa ke ciki wanda wannan alama ce babba da ke nuna al’amura za su sauya.