✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hukumar Shari’a ta dakatar da alkali kan yanke hukunci ta hanyar da ba ta dace ba

NJC takafa kwamitoci domin binciken alkalai 51 kan zargin gudanar da aikinsu ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar Shari’a ta Kasa (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a S.O Falola na Babbar Kotun Jihar Osun tare da neman a yi masa ritayar dole kan laifin saba ka’idar aiki da kuma bayar da umarnin kotu ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar NJC ta kuma kafa kwamitoci 11 domin bincike kan wasu alkalai 51 da ta samu takardun korafi a kansu.

Sakataren yada labaran NUJC Soji Oye ya ce an dakatar da Falola ne sai abin da hali ya yi, a yayin da take jiran abin da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, zai yi kan shawarar ritayar dolen.

Soji Oye ya ce NJC a taronta na 104 a Abuja, ta samu Mai Shari’a S.O. Falola da lafin ba da umarnin biyan N283,174,000 ga Bankin Polaris da wata bukwar hanya.

An gano laifin nasa ne bayan takardar korafin da Bankin Polaris da wani mai suna Dapo Kolapo Olowo suka aike wa NJC kan lamarin.

An same shi da laifin ba da umarnin cire kudaden daga asusun bankin masu kara maimakon asusun wanda ake kara — ainihin wadanda umarnin ya shafa.

An kuma samu Jastis Falola da laifin sauraron shari’a mai lamba HIK/41/2018, wadda ba shi da hurumi a kai, ba tare da ya samun takardar hukuncin daga Babbar Kotun Jihar Kwara ba, kuma ba tare da takardar shaidar rajistar shari’ar a Jihar Osun ba — inda yyake da hurumi.

Soji Oye ya ce a taron NJC karo na 104 a Abuja, karkashin jagorancin Shugaban Alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya yi watsi da bukatar Gwamna Adeleke na neman rantsar da rantsar da mukaddashin babban alkalin jihar.

Gwamnan ya nemi amincewar NJC ne bayan samun korafi kan Babban Alkalin jihar, Oyebola Adepele-Ojo da kuma matsayar da majalisar jihar ta cimma na dakatar da shi.

Soji Oye ya ce a taron NJC, ta kafa kwamitoci 11 domin bincikar alkalai 51 da ta samu korafi a kansu.

Amma kuma, bisa rahoton kwamitocin binciken wasu alkalai da ta kafa a baya, ta yi watsi da korafe-korafen da aka shigar kan wasu alkalai saboda rashin hujjoji ko janyewar masu korafin.

Alkalan da aka wanke su ne Babban Alkalin Jihar Akwa Ibom, Jastis Ekaete F. F. Obot; Jastis Benson Anya na Babbar Kotun Jihar Abia; Jastis Z. B. Abubakar na Babbar Kotun Tarayya; Jastis Opufaa Ben-Whyte da kuma Augusta Uche K. Chuku na Babbar Kotun Jihar Ribas.