✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano

Wannan lamari ya faru ne wata shid bayana auren matar da mijinta na farko

An gurfanar da wata matar aure a gaban kotun Musulunci kan zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda a Jihar Kano.

Wannan lamari ya faru ne wata shida bayan auren matar mai suna Harira Muhammad Tudun Murtala da mijinta na farko mai suna Sagiru Shu’aibu Tudun Murtala.

A yayin zaman Kotun Musulunci da ke zamanta a Post Office Malam Sagiru ya shaida wa alkali cewa kasncewar ba tare suke zaune da matar tasa ba, wata rana ya je gidanta sai kawai ya iske ta tare da wani mutum a gan gadon aurensu, lamarin da ya sa ya sanar da makwabta abin da ke faruwa.

Bayan gurfana da ita a gaban kotu, Harira ta musanta cewa akwai aure tsakaninta da mijin nata na farko, lamarin da ya sa alkali ya umarce ta da yin rantsuwa da Alkur’ani, amma sai ta janye kalamanta.

A nasa bangaren, mijinta na biyu, mai suna Bello Abdullahi ’Yankaba ya shaida wa kotun cewa aurenta ya yi a kan sadaki naira dubu dari kuma wani kawunta mai suna Abdullahi Umar ne waliyyin aurensu.

Bayan sauraron bayanansu, alkalin kotun, Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki, ya ba da umarnin a zurfafa bincike kan lamarin sa’annan a tsare matar da mijin nata na biyu a gidan yari, zuwar ranar 16 ga watan Mayu da za a ci gaba da sauraron shari’ar.