✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunwa ta sa ’yan Najeriya cin ganye —Ash Bello

’Yan kwadago sun bukaci gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin mai domin mutane na mutuwa saboda yunwa.

Shugaban Kungiyar ta Najeriya (NLC) Reshen Jihar Gombe, Kwamred Yusuf Ash Bello, ya bayyana cewa tsadar rayuwa ta sa ’yan Najeriya da dama sun koma cin ganye domin su rayu a cikin kasarsu. 

Da yake jawabi gabanin mika sakon uwar kungiyar ga gwamnan jihar a babban filin wasa na unguwar Pantami da ke fadar jihar, Kwamred Yusuf Ash Bello, ya ce kiransu ga gwamnatin tarayya shi ne a dawo da tallafi domin mutane na mutuwa saboda yunwa.

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin wasu mutane ganye suke ci suke rayuwa bayan kuma su din ’yan Najeriya.

Ya kara da cewa gwamnatin ta cire tallafi ba tare da ta tanadar wa jama’a hanyar da za su samu saukin rayuwa ba, don haka suna kira a dawo da tallafi.

A cewarsa, a irin halin da ake ciki na yunwa da tsadar rayuwa ta’addanci zai iya karuwa a kasar nan domin duk wanda bai ci ya koshi ba zai iya hana kowa zaman lafiya.

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a yayin zanga-zangar gama-gari da uwar kungiyar ta gudanar a fadin kasar domin neman gwamnatin ta kawo karshen tsadar rayuwa ta kuma dawo da tallafin man fetur da ta cire.

Da yake karbar sakon a madadin gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya, mataimakin gwamnan, Manasseh Daniel Jatau, cewa ya yi babu abin da gwamnatin jiha za ta iya a kan wannan roko nasu amma za su isar da shi zuwa inda ya dace domin su ’yan aike ne.

Manasseh Jatau, ya tabbatar musu da cewa a matakin jiha gwamnati za ta yi mai yiwuwa wajen ganin ta shawo kan wasu matsalolin da suka nemi a magance musu domin gwamna Inuwa Yahaya mai jin kukan jama’ar sa ne wanda yanzu haka yana shirin fara biyan tsofaffin ma’aikata hakkokinsu na ritaya.

Ya ja kunnensu da cewa bai kamata ma’aikaci ya dogara kacokan a kan aikin gwamanti ba, kamata ya yi ya samu wata hanya musamman noman rani don kara samun hanyar kudin shiga, wanda ko babu albashi ma’aikaci zai iya rike kansa.

Wasu ma’aikata da suka halarci zanga-zangar, sun bayyana cewa idan har gwamanti ko gwamna na son su rungumi noman rani to a cire musu dangwale na zuwa aiki.

A cewarsu, ba zai yiwu su hada noma da aiki ba domin idan mutum ya rasa dangwale na kwana hudu ba zai samu albashinsa na wannan watan ba.