✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DAGA LARABA: Ruwan ‘Fiyowata’ Na Neman Ya Gagari Talaka

Wasu masu sarrafa ruwan ledar sun fara rufe kamfanoninsu

More Podcasts

Ruwan leda ya zama abin tattaunawa a tsakanin ’yan Najeriya saboda yadda ya yi tsadar da bai taba yi ba.

Wasu na ganin shi ne ruwan sha da ake samu mai dama-dama wajen tsafta, sai dai yadda yake kara tsada a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ana komawa shan  ruwa mara tsafta a wasu wuraren.

Sai dai masu sarrafa ruwan na cewa ba daga su ba ne, inda har ta kai ga wasu na rufe kamfanoninsu.

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dalilan da suka jawo hakan.

Domin sauke shirin, latsa nan