Duk da ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziki da al’ummar Najeriya ke ciki a wannan lokaci, shirye-shiryen Sallah ƙarama na ci gaba da kankama kusan a ko’ina inda mutane ke ci gaba da shirye-shirye ganin cewa sun yi bikin wannan sallah cikin farin ciki da annashuwa.
A kowane lokacin watan azumi musamman lokacin da bikin Sallah ke kara gabatowa, teloli kan shiga yanayin aiki ba ji ba gani sakamakon yawan ɗinkin sallah da jama’a ke kawo masu.
Azumin bana dai ya zo wa ’yan Najeriya cikin wani yanayi na matsin tattalin arziki da kuma tashin farashin kayayyaki.
- Hajji: Gwamnonin Kogi, Kebbi da Kano sun tallafa wa maniyyata
- Goman Karshe: Dama ta karshe ga mai neman rahamar Allah
Sai dai ko ya ya mutane ke shirin gudanar da bikin Sallah a bana, shin mutane za su yi ɗinkin sabbin kayan sallar kamar kowace shekara?
Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa teloli a bana ma, na ci gaba da cin kasuwarsu duba da yadda jama’a ke tururuwar kai ɗinkin kayan sallarsu.
Aminiya ta yi hira da teloli da dama inda kuma suka shaida mata cewa lallai azumin bana ya yi masu ba-zata, la’akari da cewa ba su yu tsammanin za su samu yawan ɗinkin da suke samu a halin yanzu ba.
Abba Umar Muhammad, wani tela ne da ke sana’arsa a unguwar Koki da ke cikin garin Kano, ya shaida mana cewa azumin bana sai hamdala, bai yi tsammanin cewa al’umma za su yi ɗinki kamar haka ba, amma sai ga shi abin mamaki duk da yanayin matsin tattalin arziki da ake ciki, mutane sun yi ɗinkin sallah da yawa.
“A baya na yi tunanin cewa ba za a samu aiki da yawa ba, amma sai ga shi, yau sama da kwana biyar na rufe karɓar ɗinki, saboda idan na ci gaba da karɓar ba lallai mutum ya samu ba.
“Na yi tunanin cewa bana ba zan yi aiki da yawa ba, saboda yanayin tsadar kaya a kasuwa kuma ga shi jama’a babu kuɗi, ban yi tsammanin cewa za a yi ɗinki kamar haka ba. Amma sai gashi kaya sun taru har sun yi mana yawa.”
Har wa yau, Idris Adamu, wani matashin tela ya bayyana cewa, duk da tsadar rayuwa da ake ci fa, mutane suna kukutawa suna yin dinki, “kai ka san Sallah ai Sallah ce, duk halin da ake ciki ko yaya ne dole mutum zai matse ya yi.
Halliru Umar Muhammad, shi ma a nasa bangaren, ya bayyana cewa, “gaskiya na ɗinka kaya da yawa a bana kuma, ba na tunanin zan iya kammala duk kayan da suke gabana kafin Sallah, amma zan yi ƙoƙari na tsara yadda kowa zai samu wanda zai je idi da shi.”
“Wasu sun kawo kaya sama da kala biyar, wasu kuma biyu, wasu uku, wasu kuma ɗaya ma kawai, amma dai ka ga ai dole na tsara yadda kowa zai samu ko yaya ne.”
Sai dai a ɓangare guda kuma, Rabi’u Tela, matashin mai ɗinki a unguwar Gandun Sarki, ya ce, a gaskiya shi dai idan ya kwatanta bara ta fi bana, saboda ya ce a bara tun kafin a fara azumi sun riga sun rufe karɓar ɗinkin sallah.
“Ai ba haɗi tsakanin bara da bana, a bara tun kafin azumi shagonmu mun riga da mun rufe karɓar aikin sallah, kuma a hakan ba mu iya yi wa kowa ɗinkinsa gaba ɗaya ba, amma bana fa, duk da a yanzu mun rufe karɓar ɗinkin, akwai shagunan da har yanzu suna karɓa.
“Mutane ne na son sanya kayan sallah, amma matsalar yanzu ta abinci a ke wanda ya yi tsada, mutane da dama na son ɗinkin amma sun hakura saboda tsadar kayan.
“Mun yi tunanin, ko idan an yi albashi za a ga canji sai ga shi mutane musamman ’yan albashi ba ta kaya suke yi ba.
Da Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin daidaikun mutane, Musa Ibrahim Umar, ya bayyana cewa, “ai dole mu matse mu yi dinkin sallah, kayan sallah ai suna da matuƙar muhimmancin, musamman ga mata da yara.
“Na tanadi kayan sallah na tun kusan wata biyu kafin azumi ma, saboda na san abu ne wanda ya ke dole sai an yi, to kaga masu ƙaramin hali, dole mu shirya da wuri, saboda an ce mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka.
“Duk da kayan sun yi masifar tsada, na samu na yi mana kala biyu-biyu ni da iyali na, amma fa gaskiya na kashe kuɗi.
Sai dai Salisu dan kasuwa a Kofar Wambai ya bayyana cewa shi fa yanzu ba ta kayan sallah yake ba tukun, neman kuɗi yanzu ya sa a gaba amma dai kafin sallar zai yi ƙoƙari ya samu lokaci ya kai ɗinkin.
“Ba zan ce ba zan yi ɗinkin sallah ba, amma ni gaskiya yanzu lokacin da zan je na sayo kayan na kai wurin ɗinki shi ne matsala ta, ba wai ba ni da kuɗin ba ne, a’a kawai lokacin ne matsalata, amma na tabbatar wa telana cewa zan samu lokaci na kai masa kuma ya ce ba damuwa, zai kukuta ya yi mani. To kaga ai bani da matsala,” a cewar Salisu.