✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: Gwamnonin Kogi, Kebbi da Kano sun tallafa wa maniyyata

Gwamnonin sun tallafa wa maniyyatan ne sakamakon tashi da kuɗin kujerar aikin hajjin bana ta yi.

Gwamnonin Kogi, Kebbi da Jihar Kano sun tallafa wa maniyyatan jihohinsu da cikon kuɗin aikin hajji, sakamakon tashi da kujerar ya yi bana.

Babban sakataren yada labaran gwamnan Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya tabbatar wa da Aminiya, inda ya ce “Gwamnan ya bayar da umarnin a biya cikon kudin aikin hajjin maniyyata da ya yi saura.”

Ya kara da cewa, bana ana sa ran mutum 4,875 za su sauke farali daga jihar.

Mai bai wa gwamnan Kogi shawara kan harkar yada labarai, ya ce, “Gwamnatin Jihar Kogi ta biya Naira Miliyan 800, cikon kudin aikin Hajji da ya kamata maniyyata 460 su cika”.

Ya ce, hukumar jin dadin alhazai ta jihar, ta kammala biyan kudin ta hanyar wani shiri da ta yi da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON).

Ita kuwa gwamnatin Jihar Kano ta tallafa wa maniyyata 2,096 da Naira 500,000.

Yanzu maniyyata daga Jihar Kano za su cika Naira Miliyan 1.4 ne, maimakon Naira Miliyan 1.9, kamar yadda NAHCON ta buƙata.

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai na jihar, Alhaji Lamin Dan Baffa ne, ya bayyana haka lokacin da yake zanta wa da manema labarai a Kano.