✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yunwa ta kashe mutum 23 a sansanin ’yan gudun hijira da ke Katsina’

Yunwa, hawan jini da matsananciyar damuwa ne suka kashe su

Akalla mutum 23 ne suka rasu a sansanin ’yan gudun hijirar da ke Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina sakamakon yunwa, hawan jini da kuma matsananciyar damuwa.

Shugaban sansanin, Sa’ad Salisu ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da ’yan jarida a Jibiya ranar Litinin.

Bayanan da Kungiyar Ci Gaban Jibiya ta samu sun nuna akwai akalla mutum 22,365 da suka fito daga kauyukan Shimfida da Garin Maiwuya da Garin Zango da Garin Kwari (Farfaru) da kuma Tsambaye, wadanda a yanzu suke zaune a garin na Jibiya.

Mutanen dai na samun mafaka ne a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Jibiya.

Sa’ad Salisu, wanda har ila yau shi ne Shugaban Kungiyar Ci Gaban Matasan garin Shimfida, ya kuma ce akalla mata 35 ne suka haihu a sansanin a cikin watanni hudun da suka gabata, inda ya ce adadin ma zai iya wuce haka.

Shugaban ya ce babban abin da ya fi ci musu tuwo a kwarya shi ne akasarin yaran da ke sansanin ba sa iya zuwa makaranta.

“Muna da yara sama da 3,000 a wannan sansanin da suka baro kauyukansu da kayan makaranta a jikinsu, amma yanzu ba sa zuwa makarantar saboda gwamnati ba ta samar musu ba.”

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta kara azama wajen dawo da zaman lafiya a yankin don mutane su sami damar komawa su ci gaba da noma.

Da yake mayar da martani, Shugaban Karamar Hukumar ta Jibiya, Bishir Sabi’u, ya ce gwamnati ta samar da isassun kayan rage radadi a sansanin.

Ya ce ko a kwanakin baya ya aike musu da buhunan hatsi da dama, sannan yakan ba sansanin N200,000 kowanne mako don gudanar da harkokinsu na yau da kullum.