Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatus Sunan (JIBWIS) ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su magance matsalolin rashin tsaro, yunwa, talauci da rashin aikin yi da suka addabi al’ummar Najeriya.
Kungiyar ta kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta dawo da tallafin mai da ta janye, wanda ake alakantawa da matsalolin tsadar rayuwa a kasar a halin yanzu.
Shugaba kungiyar JIBWIS na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya ce yana da muhimmanci “a dawo da tallafin mai tare da soke duk tsare-tsaren gwamnati da suka haifar da koma-bayan tattalin arziki da sauran matsalolin da al’ummar Najeriya suke ciki.”
Sheikh Jingir ya kuma bukaci gwamnati ta kara zage damtse wajen “farfado da harkar noma wanda shi ne bangaren da ya fi samar da abin dogaro da kuma wadata kasa da abinci.”
Shehun malamin ya yi wannan kira ne a wurin rufe taron karawa juna sani kan shugabanci domin samar da cigaban al’umma, wanda kungiyar ta JIBWIS ta gudanar a garin Jos, Jihar Filato.
Duk da haka ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa sauraron jama’a wajen janye takunkumin da kungiyar ECOWAS ta sanya wa ƙasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea saboda juyin mulki da sojojin kasashen suka yi wa zababbun shugabannin siyasa.
A karshe Sheikh Jingir ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su hada kai kuma su dauki azumi da zarar an ga wata, yana mai yi musu fatan dacewa da alheran watan Ramadan mai albarka.